Kasar Sin na goyon bayan aikin kwaskwarima game da tsarin kwamitin sulhun MDD, da kuma fatan ganin an baiwa kasashe masu tasowa karin wakilci, da ikon bayyana ra'ayi.
Hakan na kunshe ne cikin kalaman kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, yayin da yake jawabi gaban mahalarta taron manema labaru da ake saba shiryawa a nan Beijing.
Mr. Hong ta kara da cewa aiwatar da kwaskwarima a tsarin kwamitin tsaron MDD ya shafi fannoni da dama, wanda hakan ke da alaka da bunkasar MDD cikin tsahon lokaci, da kuma moriyar dukkan kasashe mambobinta.
Ya ce har kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka game da burin cimma daidaito kan batutuwa daban daban, ta hanyar shawarwari bisa dimokuradiyya, wanda kuma sassa daban daban ke halarta, matakin da ya kasance tamkar ainihin burin kasar Sin dangane da yi wa kwamitin sulhun gyaran fuska.
Kaza lika kasar Sin na kallon MDD a matsayin wata babbar hukuma. Don hakan baya ga aiwatar da kwaskwarima ga kwamitin sulhun, MDDr na bukatar gudanar da gyare-gyare a fannonin zamantakewar al'ummar kasashen duniya da batun samar da ci gaba. (Tasallah Yuan)