in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun kubutar da mata da kananan yara daga hannun mayakan Boko Haram
2015-09-15 19:12:27 cri

Rahotannin daga Najeriya na cewa, dakarun kasar sun yi nasarar kubutar da mata da kananan yara da dama daga hannun mayakan Boko Haram a yayin wani samame da suka kaddamar a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojan kasa ta Najeriya kanar Sani Usman Kukasheka ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, sojojin sun yi nasara kawar da sansanonin Boko Haram da ke Banki, Kunshe da kuma yankin Bama a jihar Borno, baya ga wata gada mai muhimmanci da ta hade garuruwan Miyanti da Banki da sojojin suka kwato.

Sanarwar ta ce, sojojin za su ci gaba da yin luguden wuta ta sama da kasa har sai sun kakkabe 'yan ta'addan baki daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China