in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamaru ta dakile wani hari na Boko Haram a arewacin yankinta
2015-09-15 09:28:28 cri

Sojojin kasar Kamaru sun yi nasarar dakile wani harin 'yan kungiyar Boko Haram a yankin Balgaram dake arewaci mai nisa na kasar, kuma yake kan iyaka da Nigeriya.

Yan kungiyar masu yawa da suka yi niyyar mamaye yankin domin kai harin suna kisan fararen hula, sojojin sun samu nasarar dakile su nan take kamar yadda wata majiya ta tabbatar wa Xinhua, inda aka ce an ga gawawwakin mutane 3 daga cikin su a safiyar Lahadi.

Wannan harin ya zo ne kwana daya da Janar Bouba Dobekreo karban mukamin kwamandan sojin hadin gwiwwa da suka kunshi sojojin kasashen tabkin Chadi domin yakar kungiyar ta Boko Haram. Yanzu haka ya maida ofishin shi a yankin arewa mai nisa na kasar, inda wassu hare-haren kunar bakin waken har sau biyu suka auku a unguwar Kolofata.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China