Rahotanni daga jihar Adamawa ta Tarayyar Najeriya ya tabbatar da cewa, wani bam ya fashe a wani sansanin 'yan gudun hijira a unguwar Malkohi dake cikin garin Yola babban birnin jihar jiya Jumma'a ranar 11 ga wata, kamar yadda kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA Sani Datti ya sanar.
A wannan hadarin, mutane 7 sun halaka sannan wassu mutane 20 sun samu rauni, amma 7 daga cikinsu har an sallame su sauran 13 da suka hada da ma'aikatan bada agajin guda 4 suna karbar jinya a asibitocin cikin garin.
Kakakin na NEMA ya yi bayanin cewa, an dasa bam din ne a cikin sansanin wanda ke dauke da 'yan gudun hijira da suka dawo daga kasar Kamaru da kuma wadanda suke tsere daga jihar Borno bisa dalilin rikicin Boko Haram.
Wannan hadarin na ranar Jumma'a shi ne irinsa a karon farko da ya faru a sansanonin 'yan gudun hijira wadanda suka rasa muhallansu dalilin rikicin Boko Haram da ake fama da shi a kasar cikin shekaru 6 da suka gabata.(Fatimah Jibril)