in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeria za ta sake gina wuraren da Boko Haram ta yi wa ta'adi
2015-09-02 09:48:07 cri

Gwamnatin Nigeriya tana shirin sake gina wuraren da kungiyar Boko Haram ta yi wa ta'adi domin farfadowa daga hare haren kungiyar, in ji kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar NEMA Sani Datti.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Sani Datti ya ce, sake gina garurruwan yana da muhimmanci, ganin yadda aka kwato wuraren daga hannun 'yan kungiyar a baya bayan nan, tare da kuma la'akari da yawan 'yan gudun hijira da suka dawo daga kasar Kamaru da Jamhuriyar Niger wanda ya sa shirin da ake da shi a da na kai agajin gaggawa ya canza zuwa sake gina kauyukan, da ma ba da kwarin gwiwwa ga al'umman wajen.

Kakakin na NEMA ya ce, za'a yi wannan aiki ne cikin hadin gwiwwa da MDD, da kuma ofisoshin NEMA na jihohi, wanda ya ce, yanzu haka ana yin nazarin wuraren da za su amfana da taimakon, a cewar shi, adadin asara da lalacewar wurare a jihohin arewa maso gabashi na Borno, Adamawa, da Yobe, shi ma ana kan lissafin shi. A yanzu haka kusan mutanen dake gudun hijira a kasashen Kamaru, Niger da Chadi sun kai 57,743. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China