A ranar Asabar din da ta gabata ne wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai wa tawagar babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar, Tukur Burutai hari a kauyen Faljari da ke tsakanin Mafa da Dikwa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriyar Kanar Sani Usman Kukasheka, ta ce an kai harin ne a kan wasu daga cikin sojojin da ke tawagar hafsan wadanda suka wuce gaba.
Sai dai kuma sanarwar, ta ce, maharan ba su ji da dadi ba a hannun sojojin a inda sojojin suka kashe 'yan kungiyar har mutane 10, suka kuma kama guda 5 a raye.
Sanarwar ta kara da cewa, soja daya ya rasa ransa a lokacin gumurzun, sannan wasu guda 4 sun jikkata.
A ranar Asabar din ne hafsan sojojin Laftanar Janar, Tukur Burutai ya ziyarci sansanonin rundunonin sojin da ke yaki da Boko Haram wadanda ke a garuruwan Mafa da Dikwa.
A makonnin baya ne dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da wa'adin watanni uku ga sojan kasar da su kawar da kungiyar Boko Haram daga kasar. (Ahmad Fagam)