Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa, wasu tagwayen bama bamai da suka tashi a garin Kolofata dake yankin arewa mai nisa, sun hallaka mutane 10, tare da jikkata wasu mutanen 14.
Ministan sadarwar kasar Issa Tchiroma Bakary, ya shaidawa majiyarmu cewa, ana zargin wasu 'yara su biyu 'yan kimanin shekaru 14 zuwa 16 'yan kungiyar Boko Haram da kaddamar da hare-haren kunar bakin waken na safiyar ranar Lahadi.
Kaza lika wasu majiyoyin yankin da lamarin ya auku, sun ce, bam na farko ya tashi ne a unguwar "Latin", inda 'yan gudun hijirar Najeriya da dama ke samun mafaka, yayin da kuma hari na biyu ya auku a babbar kasuwar garin na Kolofata. Garin Kolofata dai na yankin arewa mai nisa ne a kan iyakar Najeriya da kasar ta Kamaru.
Ko da a ranar Alhamis 3 ga watan nan na Satumba ma dai wani bam ya fashe a garin Kerawa dake yankin arewa mai nisa, wanda kuma ya yi sanadiyyar kisan mutane sama da 40, baya ga wasu fiye da 100 da suka jikkata. (Saminu)