A yau ne aka shirya wata liyafar cin abincin rana don karrama manyan bakin da suka halarci bikin cika shekaru 70 da samun nasarar yaki da maharan Japan da kuma masu nuna ra'ayin karfi a duniya da kasar Sin ta shirya.
A jawabinsa yayin liyafar, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada cewa, zaman lafiya na da matukar samu, don haka wajibi ne a kiyaye zaman lafiya. Manufar kasar Sin ta tunawa da nasarar da Sinawa suka samu a kan maharan Japan da yaki da masu ra'ayin nuna karfi a duk fadin duniya, shi ne domin tunatar da jama'a game da muhimamncin tabbatar da zaman lafiya.
Bunkasuwar kasar Sin wani bangare ne na masu kishin zaman lafiya a duniya. Bugu da kari, kasar Sin tana fatan cewa, kasashen duniya za su koyi darasi daga tarihi kana su tsaya tsayin daka kan samun ci gaba cikin lumana, a kokarin samun kyakkyawar makoma da zaman lafiya a duniya baki daya. (Tasallah Yuan)