An fara gudanar da bikin tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan da nuna kin karfin tuwo na Fascist a babban filin Tian'anmen da karfe 10 na yau ranar 3 ga wata, inda firaministan kasar Sin Li Keqiang ya sanar da bude bikin.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wani muhimmin jawabi, inda ya nuna girmamawa ga tsofaffin sojoji da hafsoshi da jama'a Sinawa da suka bada babbar gudummawa a lokacin yakin kin harin Japan.
Hakazalika kuma, Xi Jinping ya bayyana cewa, a yakin kin harin Japan, jama'ar kasar Sin sun sadaukar da rayukansu da bada babbar gudummawa ga yakin nuna kin karfin tuwo na Fascist na duniya. Mun tuna da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan da yakin kin karfin tuwo na Fascist na duniya domin tunawa da girmama tarihi, da kuma nuna girmamawa ga mutanen da suka sadaukar da kai a yakin, da ci gaba da yin kokari wajen tabbatar da zaman lafiya, da kuma kirkiro wata kyakkyawar makoma. (Zainab)