Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin kakakin ma'aikatar tsaron kasar, Yang Yujun bayan da Shugaban kasar Xi Jinping ya yi alkawarin rage adadin sojin a lokacin gagarumin faretin sojin cika shekaru 70 na kawo karshen yakin duniya na biyu da aka yi a safiyar yau din a dandalin Tian'anmen dake birnin Beijing.
Yang ya ce wannan yunkurin musamman zai mai da hankali a kan rundunar da suke da tsaffin kayayyakin aikin soja, ma'aikatan bangaren mulki da kuma ma'aikatan da ba su aikin soji domin gyara tsarin rundunar kasar.
Ya ce rage adadin ya biyu bayan tsarin da ake da shi a yanzu na sojin kasa da halin da ake ciki a kasar. Ya kara da cewa adadin rundunar zai ragu amma kuma zai yi takara da saura kuma tsarinsu za su fi mai da hankali a kimiyya.
Wannan ne zai zama karo na hudu da kasar ta rage adadin rundunarta tun daga shekara ta 1980 wanda a lokacin take da yawan soji a duk fadin duniya na miliyan 2.3. A shekara ta 1985 kuma ta sake rage adadin da kusan miliyan 1 mafi girma a ragewa da kasar ta fuskanta. Yang Yujun ya yi bayanin cewa wannan kwaskwarima zai bi tsarin mataki mataki ne, a hankali za'a ci gaba da fitar da wassu matakan. (Fatimah Jibril)