Shugaba Xi bayan maraban da ya yi ma Mr Ban game da halartar wannan muhimmin biki na kasar, ya ce bikin ya nuna kudurin da al'ummar kasar Sin ke da shi na kiyaye zaman lafiya.
Ya shaida ma Mr Ban cewa MDD na daya daga cikin sakamako masu muhimmanci na yakin duniya na biyu, Sin ce kasar farko da ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar majalissar, kuma a shirye take na kiyaye nasarar da aka samu sakamakon yakin duniya da kuma yarjejeniyar majalissar kamar yadda aka tanada ma kasa da kasa tare.
A cewar Shugaba Xi, kasar Sin za ta nace ma yarjeniyoyin kasa da kasa tare da karfafa ayyukan majalissar, inganta ayyukanta wajen kiyaye zaman lafiya da cimma ci gaba tare, musamman wajen karfafa ayyukan shi na kiyaye zaman lafiya da kuma cimma kudurin muradanta bayan shekara ta 2015.
A nashi bangaren Mr Ban Ki-Moon ya ce al'ummar kasar Sin sun yi asara da dama a lokacin kuma sun mika babban gudunmawa wajen yaki da masu ra'ayin nuna karfin tuwo kuma bikin ya nuna yadda al'ummar kasar suke da burin ganin zaman lafiya.
Ya lura da cewar a cikin shekaru masu yawa, Sin ta shiga cikin ayyukan kiyaye zaman lafiya da ci gaba da dama, musamman na MDD, al'ammuran masu tsanani na yankuna da kuma ayyukan hadin gwiwwa na kudu maso kudu. (Fatimah Jibril)