in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar yayin bikin tunawa da samun nasarar kawo karshen harin fin karfi na Japanawa shekaru 70 da suka gabata
2015-09-03 11:56:15 cri

Ya 'yan uwana alummar kasar Sin maza da mata

masu girma shugabannin bangarorin gwamnati da wakilan MDD da sauran kungiyoyi na duniya

masu girma manyan baki

masu girma jami'an sojoji da suka halarci wannan fareti

maza da mata 'yan uwa da abokan arziki

ina yi muku barka da zuwa.

Wannan wata muhimmiyar rana ce da al'ummar duniya ba za su taba mantawa da ita ba. A yau shekaru 70 ke nan cif cif da al'ummar kasar Sin suka yi gumurzu har na tsawon shekaru 14 kuma aka samu nasara na yakar harin fin karfi wanda ya tabbatar da kawo karshen yakin zaluncin Japan, kuma tun daga waccan rana ce duniya baki daya ta samu haske na zaman lafiya.

Zan yi amfani da wannan dama a madadin babban kwamitin koli na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, da Wakilin zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kasar Sin, da zaunannun wakilan ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin, da babban kwamitin lura da al'amurran sojoji na kasar Sin, ina mika godiya tare da yin jinjina ga illahirin dakaru sojoji 'yan mazan jiya da 'yan kasa na gari wadanda suka sadaukar da rayukansu a lokacin yakin, kai har ma da sauran al'ummar Sinawa dake ciki da wajen kasar wadanda suka taimaka wajen tabbatar da samun nasara a wancan yaki. Ka zalika ina mika godiya ta musamman ga abokan huldarmu gwamnatocin kasashen waje wadanda suka bada gudumowarsu ga al'ummar kasar Sin a wanann yaki. Kuma ina yi wa dukkannin wakilai da baki daga kasashen ketare, da wakilan sojoji daga kasashen waje wadanda suka samu damar halartar wananan biki a wannan rana.

Maza da mata 'yan uwa da abokan arziki,

Yakin da al'ummar Sin ta gudanar na kin jinin harin fin karfi na Japanawa wanda duniya ta kyamace shi, yaki ne tsakanin zalunci da tabbatar da adalci, tsakanin duhu da haske, kuma yaki ne tsakanin koma baya da kawo ci gaba. A wancan kazamin yaki, wato ina nufin yakin da al'ummar Sinawa suka tunkara na kin zaluncin Japanawa, yakin ya dauki lokaci mai tsawo, kuma al'ummar Sinawa sun sadaukar da kansu a wannan yaki amma daga karshe an yi galaba ta hanyar amfani da karfin tuwo wajen yakar zaluncin Japanawa domin tabbatar da ci gaba da kare dadadden tarihin Sinawa na shekaru dubu 5 da kuma tabbatar da zaman lafiyar dan adama. Wananan gagarumar nasara da al'ummar kasar Sin ta samu wani babban shafi ne a tarihin yaki.

Wannan nasara da kasar Sin ta samu a yakin kin zaluncin Japanawa shi ne cikakken tarihin samun nasara na farko a yakin da kasar Sin ta yi na kokarin kare kanta daga hare hare daga kasashen waje.

Wananna gagarumar nasara, ta dakile yunkurin makarkashiyar da mayakan gwamnatin Japan suka shirya na yunkurin aiwatar da mulkin mallaka kan kasar Sin, sai dai wananan yunkuri nasu bai kai ga nasara ba, sakamakon taron dangi da Japan ta fuskanta a wancan lokaci.

Wananan gagarumar nasara ta kafa wani shafi a babin tarihi kuma ta tabbatar da kasar Sin a matsayin wata babbar kasa wacce take mutunta zaman lafiya a duniya. Wannan gagarumar nasara ta samar da wata kyakyawar makoma ga kasar Sin kuma ta sake daga martabar kasar a yunkurin da kasar ke yi na kare matsayinta na kasa mai dadadden tarihi.

A lokacin yakin duniya na 2, al'ummar Sinawa sun sadaukar da kai tare da zage damtse a daukacin harkokin da suka shafi gabashin duniya, game da nuna adawa ga yakin nuna karfin tuwo, hakan ya sanya mu bada gagarumar gudummawa wajen cimma nasarar da aka samu.

Yayin yakin da suka yi da harin kin jinin maharan Japan, Sinawa sun samu babban goyon baya daga kasa da kasa. Sinawa za su ci gaba da tunawa da gudummawar al'ummun kasashen da suka ba su taimako, har aka kai ga samun nasarar yakin nuna karfin tuwo.

Maza da mata

'Yan uwa da abokan arziki

Darasin dake kunshe cikin yakin duniya ya sanya al'umma kara martaba zaman lafiya. Don haka dalilinmu na wannan bikin cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin jinin maharan Japan, da kuma yakin duniya na nuna kyamar amfani da karfin tuwo shi ne, tabbatar da tarihi cikin zukatanmu, da martaba wadanda duk suka rasa rayukansu bisa wannan manufa, tare da kuma kara martaba kimar zaman lafiya da inganta makoma ta gaba.

Yakin da ya gudana ya haddasa babbar barna a nahiyoyin Asiya, da Turai, da Afirka, da yankunan Oceania, yaki ne da ya jefa sama da mutane miliyan 100 cikin masifa, inda Sin miliyan 35 suka rasu ko suka jikkata. Ita ma Tarayyar Soviet ta rasa mutane da yawansu ya zarta miliyan 27. Hanya mafi dacewa ta martaba wadannan 'yan mazan jiya da suka sadaukar da rayukansu domin wanzar da zaman lafiya, ita ce wanzar da 'yanci, da adalci, da zaman lafiya, a kuma nuna alhini na rasuwar fararen hula da ba su ji ba su gani ba, tare da tabbatar da cewa hakan ba za ta sake aukuwa ba a nan gaba.

Yaki tamkar madubi ne. kallonsa kansa mu kara fahimtar muhimmancin zaman lafiya. A yau zaman lafiya da ci gaba sun zamo akidun duniya, sai dai duk da haka akwai sauran rina a kaba. Yaki na ci gaba da kasancewa takobi zararre dake reto a wuyan bil'adama. Don haka ya zama wajibi gare mu mu rungumi darussan dake kunshe cikin tarihi, mu kuma zage damtse wajen tabbatar da zaman lafiya.

Domin wanzar da zaman lafiya, ya dace mu yi hadin gwiwa wajen samar da duniya mai fatan cimma makoma guda. Kyama, da kiyayya, da yaki ba sa haifar da komai sai masifa da halin kunci, yayin da martaba juna, da daidaito, da zaman lafiya, da ci gaba, da kyakkyawar makoma ke matsayin ingantacciyar hanyar da ya dace a bi. Ya zama wajibi dukkanin kasashe su hada gwiwa da juna, wajen tabbatar da nasarar ka'idoji da tsare tsare wadanda ke kunshe cikin dokokin MDD, su kuma kafa wani sabon tsarin hulda kasa da kasa, wanda zai ba da damar cimma moriyar juna, da babbar nasarar wanzar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

Domin wanzar da zaman lafiya, kasar Sin za ta ci gaba neman bunkasa ta hanyar lumana. Mu Sinawa mutane ne masu kaunar zaman lafiya. Kuma duk ci gaban da kasar Sin ta samu ba za ta mamaye wata kasa ko zama barazana ko kuntatawa wata kasa ba. Burin Sinawa a kullum shi ne kulla huldar abokanta da dukkan kasashe tare da nuna sakamako ko nasarar da Sinawa suka samu kan mayakan kasar Japan da kuma masu nuna ra'ayin nuna karfi a duniya sannan da samar da babbar gudumawar da ta bayar a duniya ga ci gaban bil-Adama.

Wajibi ne kanana da manyan sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin su kwana da sanin irin nauyin da ke kansu na kare rayukan jama'a, da kare 'yanci da tsaron kasa da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya. Don haka a nan ina son na yi amfani da wannan dama don sanar da cewa, kasar Sin za ta rage yawan sojojinta dubu 300.

Maza da mata

'Yan uwa da abokan arziki

Kamar yadda wani karin maganar Sinawa ke cewa, "Bayan da aka samu sakamako a farko, kamata ya yi mu tabbatar da cewa, kwalli ta biya kudin sabulu" Jan aikin da ke gabanmu na gina sabuwar kasar Sin, yana bukatar sadaukarwar zuriya bayan zuriya. Bayan da muka shafe sama da shekaru 5,000 na wayin kai, babu tantama kasar Sin za ta kara samun makoma mai haske a nan gaba.

Ci gaban da aka samu karkashin JKS, a matsayinmu na al'umma mai kabilu daban-daban a cikin wannan kasa, kamata ya yi mu yada ra'ayin Markisanci na Lenin, muhimmacin wadannan tunani guda 3 sun kasance jagora ga sakamakon da muka samu a fannin kimmiya da kuma ci gaba. Kamata ya yi mu bi tafarkin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin, a kokarin da muke na cimma burinmu a fannonin zurfafa gyare-gyare, cusa ra'ayin kishin kasa da nuna turjiya ga duk wani hari daga ketare kana mu himmatu wajen ganin mun cimma burin da muka sanya a gaba.

Kamata ya yi mu yi la'akari da cewa, tarihi gaskiya ne. Kuma gaskiya a kullum za ta yi halinta, zaman lafiya zai tabbata. Kuma jama'a za su tabbatar da hakan. (Ahmad Fagam, Saminu Hassan, Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China