Shugaban kasar Sin ya bayyana a gun bikin tunawa da ranar cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan a yau Alhamis cewa, yaki ya kasance tamkar wani madubi, wanda ya sa aka darajanta zaman lafiya.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da neman bunkasuwa cikin lumana domin kiyaye zaman lafiya. Al'ummar Sin ta kaunaci zaman lafiya a tarihi. Ko a karkashin wane irin hali, kasar Sin ba za ta nemi mallake duniya ba, kuma ba za ta nuna karfin tuwo kamar yadda aka yi mata a lokacin da ga sauran al'ummomin duniya ba. Jama'ar Sin za su kare huldar zumunta dake tsakaninta da jama'ar sauran kasashen duniya, kana za su kiyaye nasarar da aka samu a lokacin yankin kin harin Japan da kokarin kara ba da gundummawa ga bil Adam.
Bugu da kari, shugaba Xi ya sanar da cewa, za a rage sojojin Sin dubu 300. (Lami)