Mr. Li Keqiang ya bayyana cewa, huldar abokantaka dake tsakanin kasashen Sin da Rasha bisa manyan tsare-tsare ta samu bunkasuwa cikin yanayi kyau, kasashen biyu sun taimakawa juna a fannin tattalin arziki, kuma suna da makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa a nan gaba.
A nasa bangare, Vladimir Putin ya ce, kasashen Sin da Rasha sun yi imani da juna a fannin siyasa, kuma suna cimma matsaya daya kan manyan batutuwan kasa da kasa ciki har da sakamakon da aka samu wajen yaki da ra'ayin nuna karfin tuwo a duniya.(Lami)