Ranar 3 ga watan Satumba rana ce ta cika shekaru 70 da cimma nasarar yaki da harin Japan ta jama'ar kasar Sin, kuma kasar Sin za ta yi faretin soja da wasu jerin bukukuwan tunawa. Jakadan Afghanistan dake nan Sin Mohammad Kabir Farahi ya bayyana a kwanan baya a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta yi bikin tunawa da nasarar yaki da harin Japan domin yin kira ga kasashen duniya da su darajanta da kuma kiyaye zaman lafiyar duniya.
Mohammad Kabir Farahi ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da wakilin CRI kafin bikin tunawa da za a yi a ranar 3 ga watan Satumba. Inda ya ce, kasar Sin ta ba da babbar gundummawa wajen yaki da harin Japan, lamarin da ya gaggauta wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.(Lami)