in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun sa lura ga bikin tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan da ake gudanar a kasar Sin
2015-09-03 09:08:23 cri

Ana gudanar da bikin tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan da ake gudanar a nan birnin Beijing na kasar Sin a yau ranar 3 ga wata. A kwanakin baya, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun maida hankali sosai kan wannan biki, da watsa labaru game da ayyukan shirya bikin da kasar Sin ta yi, inda suka yi nuni da cewa, wannan biki ba ya shaida karfin kasar Sin kawai ba, hatta ma ya shaida cewa, ba za a manta da tarihin yaki ba, da sanar da yin imani da tabbatar da zaman lafiya.

Jaridar Russia NG ta bayyana cewa, a cikin shekaru 70 bayan yakin duniya na biyu, ba a girmama matsayi da muhimmiyar rawar da kasar Sin ta taka a yaki da Fascist ba. A hakika dai, a sakamakon yakin da kasar Sin ta yi da mayakan Japan, Japan da Jamus ba su iya yin hadin gwiwa da juna ba. Yanzu kasar Sin tana shirya da gudanar da bikin tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar kin harin Japan. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da sauran shugabannin kasa da kasa za su halarci bikin bisa gayyatar da aka yi musu. Manufar wannan bikin shi ne domin nuna karfin kasar Sin da kuma burin shimfida zaman lafiya na shugabannin kasa da kasa.

Jaridar WallStreet Journal ta kasar Amurka ta bayyana cewa, a yakin nuna kin karfin tuwo na Fascist a duniya, kasar Sin ta riga kawacen kasashen yammacin duniya shiga yakin, domin sojojin Japan sun fara kai hari ga kasar Sin tun daga shekarar 1937. Ban da tunawa da cimma nasarar yakin kin harin Japan, bikin zai shaida sadaukar da kai da babbar gudummawar da kasar Sin ta bayar wajen yaki da Fascist.

Jaridar Pyramid daily ta kasar Masar ta bayyana cewa, za a yi gagarumin bikin faretin soja a kasar Sin a wannan karo, ciki har da sojojin kasashen waje da tawagar tsofaffin sojoji da suka shiga yakin duniya na biyu. An horar da dukkan sojojin da za su halarci faretin, kuma an cimma nasarar gwajin yin faretin soja a kwanakin baya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China