in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Uganda sun yi shawarwari a tsakaninsu
2015-03-31 20:37:00 cri

A Talatar nan ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya tattauna da takwaransa na kasar Uganda Yoweri Museveni a nan birnin Beijing, inda shugabannin biyu suka jinjinawa dankon zumunci, da hadin gwiwar da ke tsakaninsu, matakin dake tallafawa burin cimma moriyar juna.

A yayin ganawar, shugabannin 2 sun kuma amince da amfani da dukkanin zarafi, wajen raya huldar da ke tsakanin kasashen 2, ta yadda za su zamo misali a sabon salon huldar abota, mai kunshe da daidaito, da amincewa juna, tare da yin hadin gwiwar neman nasara tare.

Kazalika kasashen biyu na fatan kara azama tare, a fannin bunkasa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da daukacin kasashen Afirka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China