in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Uganda ya kori fairaministansa
2014-09-20 16:23:14 cri
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya kori faraministan kasar Amama Mbabazi a ranar Jumma'a bisa wani matakin da ya baiwa al'ummar wannan kasa dake gabashin Afrika.

Mista Museveni ya aikewa shugabar majalisar dokokin kasar, madam Rebecca Kadaga da wata wasika, inda ya sanar da ita da matakinsa na tunbuke mista Mbabazi daga mukaminsa.

Na dauki niyya, bisa aiwatarwa nan take, da kuma nada Ruhakana Rungunda a matsayin sabon fiaraministan kasar Uganda in ji shugaba Museveni, a cikin wata sanarwa ta fadar shugaban kasar da aka fitar a Kampala.

Kafin ya kai ga mukamin faraminsta, mista Rugunda ya rike kujerar ministan kiwon lafiya da kuma wakilin dindindin na kasarsa a MDD daga watan Janairun shekarar 2009 zuwa watan Mayun shekarar 2011. Haka kuma shi ne daya dagada cikin ministocin kasar da ya samu wa'adin aiki mafi tsawo tun zuwan Meseveni kan karagar mulkin kasar Uganda a shekarar 1986.

Jita jita na bayyana sabanin dake tsakanin Museveni da Mbabazi bisa dalilin cewa shi mista Mbabazi ya bayyana sha'awarsa na shiga takarar shugaban kasa a shekarar 2016 a matsayin dan takarar jam'iyyar NRM mai mulki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China