in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan kasar Uganda sun dakile harin ta'addanci
2014-09-14 16:13:33 cri
Kakakin rundunar 'yan sandan kasar Uganda Fred Enanga ya ce rundunar ta samu nasarar dakile wani harin ta'addanci da wasu mahara suka shirya kaddamarwa a Kampala fadar gwamnatin kasar.

Enanga wanda ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarun kasar Sin hakan ta wayar tarho, ya kara da cewa jami'an tsaron sun kuma cafke wasu wadanda ake zargi da hannu, cikin shirya wannan ta'asa a jiya Asabar.

Tun da fari dai ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar ta Uganda ya fidda wata sanarwa kan shafin sa na yanar gizo, wadda ke gargadin Amurkawan dake kasar da su kauracewa zirga-zirga, su kuma tabbatar sun kasance a wuraren dake da cikakken tsaro.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China