in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Uganda na sa ran tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa da Sin ke ginawa a kasar za ta amfanawa jama'arsa
2015-07-29 12:13:16 cri
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya bayyana a ranar Litinin cewa, gwamnatin kasar Sin ta samar da babban taimako ga kasar Uganda domin raya aikin samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa a kasar, haka kuma, yana fatan tashar samar da wutar lantarkin bisa karfin ruwa ta Isimba da kasar Sin ke ginawa a kasar Uganda za ta amfanawa jama'ar kasar yadda ya kamata.

A yayin bikin kaddamar da aikin gina tashar da aka yi a wannan rana, shugaba Museveni ya bayyana godiya sosai ga gwamnatin kasar Sin kan babban taimakon da ta samar wajen raya aikin samar da wutar lantarki mai amfani da karfin ruwa a kasar Uganda. Yana imani cewa, tashar ta Isimba za ta sassauta matsalar karancin wutar lantarki da ake fama da ita a kasar, lamarin da zai taimakawa kasar wajen raya masana'antu da kuma kyautata zaman rayuwar al'ummomin kasar.

Rahotanni na cewa, kamfanin samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa na kasar Sin wato CWE ne ya dauki nauyin gina tashar ta Isimba da ke kasar Uganda, aikin da ake saran zai lashe dallar Amurka miliyan 568 kuma ana fatan kammalarsa a shekarar 2018. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China