Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya soki shugaban kasar Amurka Barrack Obama game da kalamansa a kan gazawar shugabannin kasashen Afrika na mutunta wa'adin mulki da kuma makalewa a kan kujera har sai mutuwa.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai tare da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a fadar gwamnatin dake Entebbe, mai tazaran kilomita 40 daga Kampala, Museveni ya ce Obama da sauran shugabannin kasashen yammacin duniya dole ne su mutunta bukatun mafi rinjaye al'umman kasashen na Afrika wadanda suka jefa kuri'un su bisa tafarkin demokuradiya lokacin zabe.
Ya ce wadanda suke dagewa a kan adadin shekarun mulki ba su yi daidai ba. Nahiyar Afrika ba wai saboda adadin mulki ya sa take koma baya ba sai domin rashin cikakken dunkulewarta waje daya, kasuwa ta bai daya, kayayyakin more rayuwa da kuma tsaro.
Mr. Yoweri Musaveni ya tabbatar da cewa, a kasarsa ta Uganda ba a amince da tsarin wa'adi ba, domin idan yana kan karagar mulki saboda al'ummar kasar suka zabe shi, to yana mulkin ne bisa amincewar al'ummarsa.
Ya yi bayanin cewa, kasar ta Uganda tana gudanar da zabukanta bayan ko wane shekaru 5, kuma al'ummar kasar na da zabi, za su yi zabensu kuma suke da 'yancin diban adadin shekarun mulki.
'yan majalissar dokokin kasar ta Uganda a shekara ta 2005 suka jefa kuri'an soke wa'adin mulkin sau biyu na shugaban kasar daga kundin tsarin mulkin kasar.(Fatimah Jibril)