Kakakin rundunar sojan sama ta kasar Nijeriya Dele Alonge wanda ya tabbatar da aukuwar hadarin ya ce, jirgin kirar Dornier-228 ya tashi daga wani sansanin soja dake jihar Kaduna a kan hanyarsa ta zuwa birnin Abuja, babban birnin kasar, kuma mutane guda 7 da ke cikin sa da suka hada da matuka jirgin da kuma makaniken jirgin sun rasu. Ya zuwa yanzu gano dukkan gawawwakin wadanda suka rasun.
Yan kwana-kwana da suka isa wurin da hadarin ya faru, sun yi nasarar kashe wutar da ta tashi, kuma ba wanda ya rasu ko jikkata baya ga mutanen da ke cikin jirgin, yanzu haka rundunar sojan kasar na binciken dalilin faduwar jirgin. (Maryam)