in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD yayi allawadai da hare haren ta'addanci a Najeriya
2015-07-18 13:10:00 cri
Babban sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya yi allawadai da babbar murya a ranar Asabar da hare haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 60 a Gombe da Damaturu dake arewa maso gabashin Najeriya, tare da kara jaddada tallafin MDD ga gwamnatin Najeriya kan kokarinta na yaki da ta'addanci.

Wadannan munanan kisan kai sun faru ne, a yayin da mutanen da hare haren suka rutsa dasu, suke sallar Idin aid el-Fitr da aka sani da karamar sallah, da ya kasance wani muhimmin lokaci ga iyalai da al'ummomi, in ji mista Ban a cikin wata sanarwa ta bakin kakakinsa da aka fitar a birnin New York, kuma ya kara da cewa, hakan ya kasance kalubale ga imani na dukkanin al'umma. Ban ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Harin ta'addanci na baya bayan nan ya faru a Damaturu, babban birnin jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, a lokacin da musulmi suke sallar Idin Aid el-Fitr, da ke kawo karshen wata mai tsarki na Ramadan bisa kalandar addinin musulunci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China