A jawabinsa na fatan alheri yayin bikin, hafsan da ke ofishin jakadancin Sin a Nijeriya Kanar Wang Runxu ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, an raya dangantakar dake tsakanin Sin da Nijeriya cikin armashi, kuma dangantakar soji tsakanin bangarorin biyu ta kara inganta. A shekarar 2014, ayarin jiragen ruwan yaki masu ba da kariya na 16 na sojojin Sin ya ziyarci Nijeriya, don kara mu'amalar soji a tsakaninsu. Kazalika, Sin ta taimakawa Nijeriya wajen horar da hafsoshin sojinta, baya ga wasu agajin inganta harkokin sojojin kasar na kai tsaye.
A sa'i daya kuma, ciniki a fannin kayayyakin soji dake tsakanin kasashen biyu ya shiga wani sabon matsayi, a shekarar 2009, Nijeriya ta sayi jiragen saman yaki kirar F-7 guda 15 daga kasar Sin, yayin da a shekarar 2015, Sin ta sayarwa Najeriya da wani jirgin ruwan sintiri, matakan da ke nuna dankon zumunci dake tsakanin sojojin kasashen biyu.
A nasa bangare kuma, wakilin babban hafsan hafsoshin Nijeriya manjo janar Edward ya jinjina mu'amalar soji da ke tsakanin kasashen biyu, kuma ya yaba wa kokarin Sin wajen raya danganatakar sojojin tsakanin kasashen biyu. Ya ce, Sin da kuma sojojinta sun zama abokan arzikin Nijeriya.(Bako)