in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane da dama sun rasu sakamakon harin Bam a kasuwar Gamboru
2015-07-31 18:59:40 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane da dama sun rasa rayukan su, sakamakon wani harin kunar bakin wake da ya auku a kasuwar garin Gamboru, dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Wata majiya ta rundunar sojin Najeriyar ta ce wata mace 'yar kunar bakin wake, dake kan wani babur mai kafa uku ce ta tada bam din dake jikin ta da sanyin safiyar Juma'ar nan, lamarin da ya sabbaba kisan mutane da dama.

Majiyar ta ce an samu asarar rayuka masu yawa kasancewar kasuwar na kusa da wata tashar mota. Kuma kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da harin, koda yake sau da dama akan danganta irin wadannan hare-hare da kungiyar Boko Haram.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China