A gun taron, jakadan Sin a Nijeriya, Gu Xiaojie ya yi jawabi, inda ya waiwayi yanayin da ake ciki a Nijeriya a farkon rabin shekarar bana a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da kuma tsaro, tare da yin nazari kan sabbin matakan da aka dauka a fannonin tsaron kasa, da yaki da cin hanci da rashawa da kuma raya tattalin arziki a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari. Jakada Gu ya ce, sabuwar gwamnatin kasar Nijeriya za ta kafa majalisar ministoci nan ba da dadewa ba, daga bisani za ta gabatar da sabbin manufofi da cika alkawarinta na yin gyare-gyare a kasar. A sabili da haka, jakada Gu ya sa kaimi ga kamfanonin Sin a Nijeriya da su yi imani cewa, akwai makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da gudanar da ayyukansu bisa doka.(Fatima)