in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun cimma nasarar kubutar da mutane 178
2015-08-03 13:41:13 cri
Rundunar sojin Nijeriya ta fidda wata sanarwa a jiya Lahadi, wadda ke cewa ta samu nasarar kubutar da mutane 178 wadanda mayakan Boko Haram ke garkuwa da su, cikin matakan da rundunar ke dauka a baya bayan nan.

Kakakin rundunar sojojin Nijeriyar ne ya bayyana hakan cikin sanarwa, inda ya ce an kaddamar da wasu hare-haren sojin ne a wani wuri mai nisan kilomita 70, a kudu maso gabashin birnin Maiduguri dake tarayyar Najeriya, kuma mutanen da aka ceto sun hada da yara kanana 101, da mata 67.

Har wa yau kuma matakin sojin da dakarun kasar ke dauka ya bada damar murkushe sansanonin kungiyar Boko Haram da dama, tare da kame wani kwamandan kungiyar guda daya, ko da yake rundunar sojin ba ta bayyana lokacin da aka kaddamar da hare-haren ba.

Tun dai cikin shekarar 2004 ne kungiyar Boko Haram ta fara kaddamar da hare-haren ta'addanci a wurare daban daban, ciki hadda wuraren dake kan iyakar Nijeriya da yankin arewacin kasar Kamaru.

Bisa kididdiga, daga shekarar 2009 zuwa yanzu kungiyar Boko Haram ta kashe mutane a kalla dubu 15. A kuma watan Febrairun bana kasashen Nijeriya, da Kamaru, da Nijer da Chadi suka kafa wata rundunar soji ta kasa da kasa mai kunshe da sojoji 8700, don daukar matakan soji kan kungiyar ta Boko Haram.

Kafin hakan, cikin watan Maris na bana, kungiyar Boko Haram ta sanar da yin mubaya'a ga kungiyar IS. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China