Madam Hua ta furta cewa, tun asali kasar Sin ke da mallakar tsibirin Diaoyu, don haka take kalubalantar Japan da ta daina duk ayyukan mamaye ikon mallakar cikakken yankin kasa na Sin.
Ban da haka, madam Hua ta jaddada cewa, kowace hanyar da Japan za ta bi domin yada jita-jita, ba za a canza ainihin tarihi na cewa, tun asali Sin ce ta mallaki tsibirin Diaoyu.
Ta ce, Sin na kalubalantar Japan da ta amince da ainihin tarihi, ta daina yunkurin mallakar cikakken yankin kasar Sin. (Fatima Liu)