Taron wanda ya gudana a nan Beijing ya yi matukar jawo hankalin sassan daban daban na duniya.
Cikin sharhin da kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua ya wallafa game da hakan, ya ce, matsayar da aka cimma a fannonin hudu na da matukar muhimmanci ga burin kyautata, tare da bunkasa dangantaka tsakanin Sin da Japan.
Sharhin ya kuma yi fatan Japan za ta aiwatar da sharuddan da aka cimma, game da yunkurin samun amincewa da juna ta fannin siyasa tsakanin kasashen biyu, da kuma sa kaimi ga bunkasa dangantaka tsakaninsu yadda ya kamata.
Kasashen duniya da dama dai sun yabi wannan mataki, suna masu daukarsa a matsayin abin da ka iya bunkasa dangantaka mai tsaho tsakanin kasashen biyu, da ma babbar moriyar al'ummunsu.
Game da hakan wani manazarci a hukumar binciken tarihin yankunan arewa da gabashin Asiya, Cha Jae-bok ya ce, yayin tattaunawar da sassan biyu suka gudanar, sun fi dora muhimmanci kan manyan fannoni, matakin da ya dace da babbar moriyar da suke fatan cimmawa. Tare da taka rawar gani wajen bunkasa dangantaka mai dorewa a tsakaninsu.(Fatima)