Madam Hua ta bayyana hakan ne a gun taron manema labaru a yayin da aka yi mata tambaya game da ra'ayin Sin kan batun ziyarar da mai dakin firaministan kasar Japan Akie Abe ta kai wurin ibadar Yasukuni nan da ake takaddama a kai a ranar 18 ga wata.
Hua ta kara da cewa, kamata ya yi kasar Japan ta waiwayi tarihinta na kai hare-haren da ta aikata, da gudanar da ayyukan kara imani da samun sulhuntawa a tsakaninta da kasashen Asiya dake makwabtaka da ita. (Zainab)