Yau Jumma'a 7 ga wata, Yang Jiechi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin ya yi shawarwari da shugaban hukumar ba da tabbaci ta fuskar tsaron kasar Japan Syotaro Yachi a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin.
A yayin shawarwarin, bangarorin 2 sun cimma ra'ayi daya a fannoni 4 dangane da yadda za a daidaita da kyautata huldar da ke tsakanin kasashen 2.
Na farko, bangarorin 2 za su bi dukkan ka'idoji da ra'ayi da aka tanada cikin takardun siyasa guda 4 da suka cimma, za su ci gaba da raya huldar da ke tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare domin samun moriyar juna.
Na biyu, bangarorin 2 sun cimma daidaito a wasu fannoni bisa ka'idar duba tarihi da fukantar makoma mai kyau yadda ya kamata dangane da yadda za a kawar da cikas ta fuskar siyasa, wanda ke kawo illa ga huldar da ke tsakaninsu.
Na uku, bangarorin 2 sun fahimci cewa, akwai bambancin ra'ayi kan tashin hankali da aka fuskanta a shekarun baya sakamakon yankin tekun Gabas na kasar Sin, ciki hada da tsibirin Diaoyu. Sun amince da hana lalacewar halin da ake ciki ta hanyar yin tattaunawa da shawarwari, tare da kafa tsarin tinkarar rikici, a kokarin hana barkewar batun ba-zata.
Na hudu, bangarorin 2 sun yarda da maido da tattaunawa a tsakaninsu ta fuskar siyasa, diplomasiyya da tsaro a mataki-mataki, a kokarin samun amincewa da juna a tsakaninsu ta fuskar siyasa.
Mista Yang ya jaddada cewa, kamata ya yi bangarorin 2 su tabbatar da harsashin da suka dasa ta fuskar siyasa wajen daidaita huldar da ke tsakaninsu bisa ka'idoji da ra'ayin da aka ambata a baya, su bi kyakkyawar manufa domin raya dangantakar da ke tsakaninsu, su daidaita batutuwan da suka jawo hankali sosai cikin hanzari ba tare da bata lokaci ba, su kuma dauki hakikanin matakai na samun amincewa da juna a tsakaninsu ta fuskar siyasa, a kokarin raya huldar da ke tsakaninsu ta hanyar da ta dace yadda ya kamata.
A nasa bangaren, mista Yachi ya ce, ka'idoji da ra'ayi da aka ambata a baya a fannonin 4 na da matukar muhimmanci. Kasar Japan tana son daukar mataki bisa yadda kasar Sin ta yi. (Tasallah)