Kakakin ya bayyana hakan ne a gun taron manema labarai da aka kira a wannan rana, inda wani dan jarida ya yi tambayar cewa, yau rana ce ta tunawa da harin da maharan kasar Japan suka fara kawo wa kasar Sin, wato a ranar 18 ga watan Satumba na shekarar 1931 Mene ne ra'ayin gwamnatin Sin kan wannan batu?
Hong Lei ya ce, harin ya kasance mafarin harin da Japan ta kawoa kasar Sin. Ana tunawa da wannan rana ce, domin tunawa da tarihi, da rashin manta wa da wannan abin kunya, a kokarin nuna ra'ayin al'ummar Sin na son zaman lafiya, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya a duniya baki daya.(Fatima)