in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci neman gafara na hakika daga kalaman Firaministan Japan
2015-08-15 14:03:48 cri
A ranar Jumma'ar nan kasar Sin ta maida martani ga firaministan kasar Japan Shinzo Abe game da kalaman shi lokacin bikin cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na 2, tana mai bukatar Japan da ta nema gafara na hakika game da kuskuren ta a baya.

Kamar yadda kakakin kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a taron manema labarai, ya kamata Japan ta yi bayani dalla dalla game da yanayin cin zarafin yaki da sojojin ta suka kaddamar a baya da kuma alhakin da ta dauka sannan ta nemi gafara na hakika ga mutanen kasashen da suka sha wahala a lokacin yakin maimakon ta rika alfahari akan laifin da ta yi cikin tarihi.

Madam Hua ta ce yakin cin zarafi da Japan ta kaddamar ya kawo mummunan sakamako ga al'ummar Sinawa da sauran kasashen yankin Asiya, kuma a ganinta dole sai an waiwayi baya yadda ya kamata tare da kallon tarihi da idon basira wannan ne tushen da aka shimfida na inganta zumunci tsakanin Japan da sauran kasashen yankin Asiya.

Dangane da hakan shi ma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Yesui ya mika takarda kan matsayin da kasar ta dauka game da hakan ga jakadan kasar Japan a nan kasar Sin Kitera Masato.

A ranar Jumma'an nan ne dai firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya bayyana cewa gwamnatocin baya na kasarsa sun riga sun nemi gafara game da laifin da kasar ta aikata lokacin yakin duniyan, amma ya zame daga mika nashi neman gafarar.

Ya kuma ce bai kamata ba Japan za ta amince zuri'an ta masu zuwa su cigaba da zama cikin masu neman gafara ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China