in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar kasa da kasa ba su ga Abe Shinzo ya tuna da laifin cin zali da kasarsa ta aikata yadda ya kamata ba
2015-08-16 14:04:55 cri
Ranar 15 ga watan Agusta, rana ce da kasar Japan ta sanar da mika wuya a yayin yakin duniya na biyu. A ran 14 ga wata, firaministan kasar Japan Abe Shinzo ya yi magana kan yakin duniya na biyu bayan shekaru 70 da suka wuce tun lokacin da aka kawo karshen yakin, cikin jawabinsa, bai ambaci laifuffukan da kasarsa ta aikata a yayin yakin ba, a maimakon haka, ya ce, bai kamata 'yan kasar da aka haifa bayan yakin duniya na biyu su roki gafara kan wannan batu ba. Dangane hakan, wasu jami'ai da kafofin watsa labaran kasa da kasa na ganin cewa, ya kamata kasar Japan ta tuna laifuffukan da ta aikata cikin tarihi yadda ya kamata, za ta iya samun mutuntawa da amincewa daga kasashen makwabtaka da kuma gamayyar kasa da kasa.

Don gane haka, babban magatakardan MDD ya bayyana ta bakin kakakinsa a ran 14 ga wata cewa, Ban Ki-moon na fatan za a iya cimma fahimtar juna a tsakanin kasashen da abin ya shafa bisa amincewa da fahimtarsu kan harkokin tarihi yadda ya kamata, ta yadda za a iya ciyar da bunkasuwar yankin gaba cikin hadin gwiwa.

Haka kuma, kasar Koriya ta Kudu tana ganin cewa, "maganar Abe" ba ta nuna tunawar kasar kan tarihi yadda ya kamata ba, wadda ta kuma bata mata rai sosai.

Haka kuma, jaridar Le Monde ta kasar Faransa ta fidda rahoton cewa, Abe Shinzo bai roki gafara ba cikin maganar nasa ba, haka kuma, ya ce, bai kamata 'yan kasar Japan da aka haifa bayan yakin duniya na biyu su dauki nauyin rokon gafara kan wannan harka ba, wasu 'yan kasar Japan ba su amince da ra'ayin Abe Shinzo game da harkokin tarihi ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China