Sin ta nuna rashin jin dadi da kakkausan murya kan ziyarar da wasu 'yan majalisar ministoci na Japan suka kai haikalin Yasukuni
A yau asabar din nan a yayin taron manema labaru, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, haikalin Yasukuni yana alamantar yakin kai hari kan kasashen ketare da masu ra'ayin nuna karfin soja na kasar Japan suka yi. Ta ce, ranar 15 ga watan Agusta rana ce da masu ra'ayin nuna karfin sojan Japan suka sanar da mika wuya ba tare da sharadi ba. Wasu manyan jami'an kasar Japan sun zabi wannan rana don yin ziyara ga haikalin Yasukuni, wurin da aka ajiye alluna da ke dauke da sunayen masu laifuffukan yakin duniya na 2 domin tunawa da su, wannan ya nuna ra'ayin kuskure mai tsanani da bangaren Japan ke da shi kan matsalolin tarihi don haka kasar Sin ta nuna rashin jin dadin ta da kakkausar murya.
Madam Hua ta kara da cewa, sai har idan kasar Japan ta amince tare da kuma yin tuba sosai kan tarihin ta na kai hari, ta haka ne kawai za ta iya fuskantar makoma na hakika. (Bilkisu)