in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 70 da samun nasarar yakin kin harin Japan a kasar Sin
2015-08-15 18:41:18 cri

Ranar 15 ga watan Agusta, rana ce ta cika shekaru 70 da kasar Japan ta mika wuya, da kuma samun nasarar yaki da ra'ayin nuna karfin soja a duniya, hakan ya sa aka gudanar da bukukuwa a sassa daban daban na kasar Sin don tunawa da wannan mihimmiyar rana.

A safiyar wannan rana , masu kishin zaman lafiya daga gida da waje sun taru a dakin tunawa da Sinawa da sojin Japan suka kashe a birnin Nanjing dake gabashin kasar Sin, don tunawa da wadannan mutane fiye da dubu 300 da aka kashe, tare da tunawa da ranar cika shekaru 70 da samun nasarar wannan yaki.

Ban da haka kuma, a wannan rana da safe, a karkarar birnin Harbin dake arewa maso gabashin Sin, an bude gidan nune-nunen shaidu da aka samu game da danyen ayyuka da rundunar soja ta kasar Japan mai lamba 731 suka yi a waccan lokaci, ciki hadda gudanar da gwaji kan jikin Sinawa dake da rai, da nazarin makaman kwayoyin cuta. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China