Kwanan baya, firaministan Japan Shinzo Abe ya yi jawabi don tunawa da zagayowar ranar cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu. Sai dai kafofin yada labaru na kasar Amurka sun yi suka kan wasu kalmominsa, kuma masanan Amurka sun yi kira ga Japan da ta kara daukar nauyi.
A ranar 15 ga wata, Madam Fang Libangqin mai fafutukar ci gaban al'umma dake birnin San Francisco ta sanar da cewa, a daidai lokacin da aka cika shekaru 70 da Japanawa da suka mika kai, an bude dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na tunawa da yakin kin harin Japan da jama'ar kasar Sin suka yi na farko a kasashen waje.
Madam Fang ta ce, kafin haka a kasashen waje, babu wani dakin nune-nunen kayayyakin tarihi irin haka, sannan Sinawa na kasashen waje ba su da masaniya sosai game da wannan tarihi, sabo da haka, gina wannan daki yana da amfani sosai.
An yi karo karon hada kudin gina wannan dakin nune nune, inda a cikin kwanaki 400, an samu kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka dubu 360.(Bako)