in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu bama bamai biyu sun hallaka mutane 50 a filin Idi
2015-07-17 18:40:28 cri
Rahotanni daga birnin Damaturun jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya, na cewa mutane 50 sun rasa rayukansu, kana wasu da dama sun jikkata, sakamakon fashewar wasu tagwayen bama bamai da sanyin safiyar Juma'ar nan, yayin da al'ummar ke tururuwa filin Idin dake Layin Gwange.

Kakakin rundunar sojin Najeriyar kanar Sani Usman, ya ce Bam din farko wanda ya tashi da misalin karfe 8 saura minti 20 na safe, ya hallaka mutane 43, yayin da na biyu wanda ya tashi mintoci 2 bayan fashewar na farkon ya hallaka mutum 7.

Usman ya kara da cewa wasu mata 'yan kunar bakin wake biyu ne suka kaddamar da harin. Ya ce harin farko wata mata ce babba ta kaddamar da shi, yayin da wata yarinya mai kimanin shekaru 10 ta tashi Bam na biyu. Sai dai wasu shaidun gani da ido sun ce babu tabbas, game da ko harin kunar bakin wake ne, ko kuma dana Bama-Baman aka yi a filin na Idi.

Wannan hari na ranar sallah dai na zuwa ne kasa da kwana guda, da aukuwar wani harin a wata kasuwa dake garin Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya, harin da shi ma ya sabbaba rasuwar mutane a kalla 25, baya ga wasu sama da 30 da suka samu raunuka.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China