Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Syria ya bayar, an ce, bisa wannan umurni, za a yi wa mutanen da suka yi gudun shiga rundunar soja da sauransu afuwa daga wannan rana. Kuma an ba da kwanaki 30 zuwa 60 ga wadanda suke gudu a cikin gida da kuma ketare, idan sun je ofishin 'yan sanda da kansu cikin lokaci, za a yi musu afuwa.
Masu fashin baki sun bayyana cewa, makasudin ba da wannan umurnin shi ne kara samun yawan sojoji a Syria. Bisa alkaluman da kungiyar sa ido kan hakkin bil'adam a Syria da aka kafa hedkwatarta a birnin London ta bayar, an ce, tun bayan barkewar rikici a Syria a watan Maris na shekarar 2011 zuwa yanzu, matasa kimanin dubu 70 sun yi gudun shiga aikin soja a kasar.
Kuma bayan barkewar rikicin Syria, shugaban kasar Bashar Assad ya sha daukar irin wannan mataki sau da dama.(Fatima)