Shugaba Bashar ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Syria ta jaddada muhimmancin yaki da ta'addanci, amma kasashen yammacin duniya ba su dora muhimmanci ga wannan batu ba. Don haka kasashen yammacin duniya ma suke fuskantar barazanar ta'addanci, har ma sun zama wurin da ake kyankyasar 'yan ta'adda.
Shugaba Bashar ya kara da cewa, gwamnatin kasar Syria ta rike da yawancin yankunan kasar, amma ya amince da cewa, yanzu kasar na fama karancin sojoji, wannan ya sa an yi watsi da wasu yankuna, inda aka tattara sojoji don bada kariya ga wasu muhimman yankunan.
Bayanai na nuna cewa, wannan ne karo na farko da shugaba Bashar ya fito fili ya sanar da cewa, kasar na fama da karancin sojoji tun bayan da rikici ya barke a kasar. (Zainab)