in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ba da lambar yabo ga rundunar sojan kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura Congo-Kinshasa
2015-08-19 21:21:23 cri
MDD ta karrama rundunar sojoji injiniya da ta likitoci rukuni na 18 da kasar Sin ta tura zuwa kasar Congo-Kinshasa da lambar yabo, ciki hada da sojoji guda 218 a garin Bukavu dake lardin Sud-Kivu na kasar, dangane da babbar gudummawar da suka bayar wajen kiyaye zaman lafiya.

Ya zuwa yanzu, rundunonin sun gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya na tsawon watanni 8 a yankin Bukavu dake gabashin kasar Congo-Kinshasa, adadin ayyukan da suka yi ya kasance a kan gaba cikin dukkanin rundunonin sojojin injiniya guda 6 da MDD ta tura zuwa kasar, gaba daya rundunar sojojin da ke aikin likitanci sun ba da jinya ga mutane 1280. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China