Kamar yadda jami'an tsaro suka tabbatar ma Xinhua, manufar hakan da dakarun suka yi shi ne don su karbe ikon garin na Goma sannan su bukaci tattaunawa da gwamnati.
Majiyar ta tabbatar da cewa daga cikin dakaru 3 da aka kame ne suka bayyana wannan shirin bayan sun fadi cewa suna karkashin wata sabuwar kungiya ne da tsohon shugaban 'yan tawaye Mbusa Nyamwhisi ya kirkiro wanda yanzu haka yake gudun hijira a kasar waje.
Gwamnan arewacin Kivu Julien Paluku yace sojojin kasar sun dakile harin yana mai cewa an kashe daya daga cikin maharan sannan aka ji ma 3 rauni, a bangaren gwamnati kuma soja daya ya mutu.(Fatimah Jirbil)