in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulmai a Kashgar sun karyata jita jitar da ake yadawa a ketare
2015-07-15 18:31:34 cri
A jiya Talata 14 ga watan nan ne wasu musulmai Sinawa mazauna birnin Kashgar dake jihar Xinjiang, suka karyata jita jitar da ake yadawa a wasu yankunan ketare, game da wai ana hana musulman Azumin watan Ramadan.

Musulmin yankin na Kashgar wadanda suka zanta da wakilin mu, sun kuma ja hankalin al'umma da su rika banbanta jita-jita da kuma abin da yake gaskiya.

Tun dai daga karshen watan Yunin da ya gabata zuwa wannan lokaci ne 'yan a-waren kungiyar East Turkestan, suka rika yada kalaman karya tare da hura wutar yaki da kasar Sin ta wasu kafofin yada labarai na wasu kasashen duniya, a wani mataki na shafawa kasar ta Sin kashin kaji.

Magoya bayan kungiyar sun rika yada zargi wai kasar Sin na nuna kyama ga wasu fannonin al'ummomi da addinai, inda suke bayyana cewa wai gwamnatin ta kasar Sin ta hana musulman dake jihar Xinjiang yin Azumin watan Ramadan, da kuma sauran abadun addinin Musulunci.

Game da wannan batu, limamin masallacin Orda Ishik, wanda ke a birnin na Kashgar a jihar Xinjiang, Abeydullah Muhammed, ya bayyana cewa tun asali gwamnati na nuna girmamawa, da ba da kariya ga rayuwar musulmai. Kuma a cewar sa kowane mutum na da ikon yanke shawarar yin azumi ko a'a.

Ban da haka, liman Muhammed ya kara da cewa, Musulunci ba addinin rikici ko nuna karfi ba ne. Kana Alkur'ani mai tsarki ya yi kira ga musulmai da su yi ayyuka masu ma'ana. Sai dai abun bakin ciki a cikin 'yan shekarun baya bayan nan, wasu 'yan ta'adda suna kashe farare hula, da mabiya wasu addinan na daban da sunan kiyaye addinin Musulunci.

Ya ce wadannan munanan ayyuka sun sabawa umurnin Alkur'ani, da manufofin addinin Musulunci baki daya. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China