A watan na azumi, wata girgizar kasa mai karfi maki 6.5 bisa ma'aunin Richter ta faru a garin Pishan dake kudancin jihar Xinjiang, wadda ta haddasa mutuwa da raunatar wasu mutane da lallata wasu gine-gine da masallatai 304. Hukumomin da abin ya shafa sun yi bincike kan yanayin masallatan, inda aka tsugunar da musulmai dubu 35 a wasu wurare na wucin gadi don su ci gaba da gudanar da harkokinsu na addini. (Zainab)