in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labarai wasu 'yan satar shiga Turkiyya wadanda 'yan sandan kasar Sin suka dawo da su gida
2015-07-17 21:40:04 cri
Tun a farkon wannan shekara ne 'yan sandan kasar Sin suka dawo da wasu gungun Sinawa gida, bayan da mutanen suka nemi satar shiga wasu kasashe ta kudu maso gabashin Asiya.

Bisa ga binciken da 'yan sanda suka yi, wadannan bakin haure galibinsu 'yan jihar Xinjiang da ke arewa maso gabashin kasar ta Sin ne, wadanda suka yi shirin zuwa kasar Turkiyya, yayin da wasunsu kuma ke fatan bi ta Turkiyya zuwa kasar Syria da Iraki, domin wai halartar "jihadi".

To, ko me ya faru gare su? Bari mu fara da wasu manoma biyu, wadanda suka fito daga kudancin jihar Xinjiang. Mutanen biyu ba su san juna ba, amma wani abu da ya zo daya tsakaninsu shi ne, dukkansu na neman satar zuwa kasar da a ganinsu wai tamkar "aljanna" ce.

To, ko yaya zaman rayuwarsu ya kasance bayan da aka kama su har kuma aka maido da su kasarsu ta asali? Domin samun karin haske, sai a kalli wannan shirin bidiyo da aka shirya. http://english.cntv.cn/2015/07/17/VIDE1437100322529315.shtml

Mehmeteli, wanda ake tsare da shi a wani gidan kurkuku dake birnin Urumqi, hedkwatar jihar Xinjiang na daya daga cikinsu. Sai dai abun da ya bambanta shi daga sauran shi ne, shi wai, yana neman halartar "jihadi" ne. Domin fahimtar cikakken labarinsa, sai a kalli wannan shirin bidiyo.

http://english.cntv.cn/2015/07/17/VIDE1437100086905800.shtml  

A wannan shekara, 'yan sandan kasar Sin sun kama wasu 'yan ta'adda da dama, da suka dawo nan kasar Sin a asirce, kuma Ekber yana daya daga cikinsu. Ekber dai ya samu horo a kasar Syria daga kungiyar nan ta East Turkestan Islamic Movement, kuma ya dawo kasar Sin ne da nufin aikata ta'addanci. Sai a kalli wannan bidiyo dangane da labarinsa. http://english.cntv.cn/2015/07/17/VIDE1437100563817901.shtml 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China