in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Xinjiang ta rage tsawon lokacin sufurin sama tsakanin Asiya da Turai
2015-07-20 09:56:09 cri
A 'yan kwanakin baya ne wasu fasinjoji kimanin su 200, suka tashi daga biranen Urumqi da Lanzhou na kasar Sin zuwa birnin St Petersburg na kasar Rasha, ta jirgin sama na farko da ya fara sufuri ta wannan yanki.

Rahotanni sun nuna cewa, wannan ce hanyar jirgin sama ta uku da aka bude daga birnin Urumqi zuwa kasashen dake nahiyar Asiya da na Turai, bayan wadda ke mikawa zuwa Dubai, da kuma hanyar dake tsakanin yankin da birnin T 'bilisi na kasar Georgia.

Bayan kafuwar wadannan sabbin hanyoyi, babu bukata fasinjoji su canza jirgi daga Moscow ko Alma-Ata. Kuma hakan na nuna cewa cikin sa'o'i 5, fasinjoji za su isa birnin St Petersburg daga birnin na Urumqi, matakin da ya rage tsawon lokaci, da yawan kudi da ake kashewa ta sufurin sama tsakanin Sin da kasashen Turai.

Jihar Xinjiang, jiha ce dake kasar Sin mafi kusa da kasashen Turai. Ta kuma kasance a matsayi na musamman, wanda hakan ya sa birnin Urumqi ya zama muhimmiyar mahadar jiragen sama ta Sin zuwa yammacin Asiya da Turai cikin gajeren lokaci.

Bisa burin hadin gwiwa, da kafa zirin raya tattalin arziki na hanyar silki, a farkon shekarar bana, hukumar zirga-zirgar jiragen saman fasinja ta Sin ta fidda wani bayani kan yadda za a sa kaimi ga bunkasa hanyar jiragen saman fasinja a jihar ta Xinjiang, inda ta kalubalanci kamfanin jaragen sama da ya kafa hanyoyin jirage daga birnin Urumqi zuwa tsakiyar Asiya, da yammacin Asiya, da kudancin Asiya, da kuma kasashen Turai da sauransu. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China