Haka kuma, hukumar kiwon lafiyar WHO ta bayyana cewa, a halin yanzu, ana sa ido kan damar samun yaduwa cutar daya tilo a kasar, inda wani matashin kasar ya rasu bayan da ya koma gidansa a garin Tonkolili dake arewancin kasar, daga Freetown, babban birnin kasar, sa'an nan bisa binciken da likita ya yi masa, an tabbatar da cewa, cutar Ebola ce ta kashe shi. Daga bisani kuma, an tabbatar da cewa mutane biyu daga iyalinsa su ma sun kamu da cutar, don haka yanzu ana ba da jinya gare su, haka kuma, an kebe mutane 43 da suka taba yin mu'amala da matashin a garinsa, da wassu 38 a birnin Freetown.
Ya zuwa yanzu, an shiga mataki na uku na aikin hana yaduwar cutar Ebola a kasar Saliyo, kuma muhimmin aiki na matakin shi ne gano ko wace hanyar da za ta iya haddasa yaduwar cutar, da kuma toshe hanyoyin cikin sauri. (Maryam)