A yayin wannan ganawa, mista Wang Yi ya taya murna ga kasar Saliyo wajen cimma nasarar yaki da cutar Ebola a karkashin jagorancin shugaba Koroma, ya yi imani cewa, kasar za ta kawar da cutar kwata kwata daga kasar tun da wuri.
Ban da haka, Wang Yi ya ce, bayan da ala shawo kan cutar Ebola da kuma lokacin da kasar Saliyo ke gudanar da tsarin neman samun ci gaba, Sin za ta ci gaban da ba da taimako da yin hadin gwiwa da Saliyo a wasu manyan fannoni biyar da suka hada da kiwon lafiya, da hakar ma'adinai da samar da makamashi, da bunkasa aikin noma da na kamun kifi, da raya manyan ayyukan more rayuwa, da kuma kara raya harkokin albarkatun kwadago da dai sauransu.
A nasa bangare, shugaba Koroma ya bayyana cewa, kasar Saliyo ba za ta iya cimma nasarar yaki da cutar Ebola cikin gajeren lokaci ba, in dai ba tare da gudummawar da kasar Sin ta samar. Wannan ya nuna cewa, Sin aminiyar Saliyo ce. Gwamnati da jama'ar kasar sun nuna godiya sosai ga shugabanni da jama'ar kasar Sin. Da fatan Sin za ta ci gaba da ba da taimako wajen farfado da kasar Saliyo bayan shawo kan cutar Ebola. Taimako da hadin gwiwa da Sin za ta yi da Saliyo a fannoni biyar sun dace da bukatun Saliyo na samun bunkasuwa. Shi ya sa, Saliyo za ta kara kokarin kaddamar da aikin tare da kasar Sin yadda ya kamata tun da wuri.(Fatima)