Mista Wang ya kasance ministan harkokin waje na wata babbar kasa a duniya da ya kai ziyara a yammacin Afrika tun bayan barkewar wannan annoba mai kisa a cikin wadannan kasashe a shekarar 2014.
Wannan mataki na kara nuna cewa kasar Sin ba ta dakatar kuma ba zata daina taimakon da take baiwa 'yan uwanta na kakasashen Afrika ba dake cikin bukata.
Jim kadan bayan barkewar annobar, kasar Sin ta kasance kasa ta farko wajen tura ma'aikatan kiwon lafiya a cikin wadannan kasashen yammacin Afrika da cutar ta fi shafa, kuma kasa ta farko da ta bada taimakon kayayyakin likitanci da na magunguna.
Domin yaki da cutar Ebola, kasar Sin ta samar da wani tallafi har sau hudu ga kasashe 13 na shiyyar da cutar ta shafa ko kasashe makwabta na darajar dalar Amurka miliyan 120.
Har zuwa wannan lokaci, Sin ta aike da jami'an kiwon lafiya fiye da dubu 13 a kasashen Saliyo, Laberiya da Guinee, har ma da wasu kasashe makwabtansu.
A bayan nan ma, kasar Sin ta dauki niyyar bada wani karin taimako na dalar Amurka miliyan 5 ga asusun abokan hulda na MDD wajen mai da martani kan annobar Ebola domin tallafawa farfadowar kasashen da cutar ta shafa.
A tsawon lokacin shiri na farfadowa, kasar Sin zata tallafawa gina wani tsarin kiwon lafiya na yaki da cututtuka a Afrika kuma zata taimakawa kasashen Afrika wajen kara kyautata karfinsu na maida martani kan matsalolin kiwon lafiya na jama'a.
A watan da ya gabata, Erastus Mwencha, mataimakin shugabar kwamitin tarayyar Afrika (AU), ya nuna godiya ga kasar Sin kan taimakon da ta bayar wajen kafa cibiyar Afrika ta yaki da cututtuka tare da jaddada cewa Afrika na fatan ganin kasar Sin ta kara himmatuwa wajen sake gina tsarin kiwon lafiya na Afrika. (Maman Ada)