in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron shugabannin SADC karo na 35 ya mai da hankali kan gaggauta bunkasuwar harkokin masana'antu
2015-08-18 10:37:00 cri
Jiya Litinin 17 ga wata, an yi taron shugabannin kungiyar raya kudancin Afirka ta SADC a babban birnin kasar Botswana, Gaborone, bisa shirin gaggauta bunkasuwar harkokin masana'antu a yankin wanda ya kasance babban taken taron.

Babbar sakatariyar kungiyar Stergomena Tax ta bayyana a yayin bude taron cewa, shugabannin kungiyar raya kudancin kasashen Afirka sun cimma matsayi daya cewa, ya kamata a dauki aikin gaggauta bunkasuwar harkokin masana'antu a matsayin abu mafi muhimmanci wajen cimma yunkurin samun dunkulewar yankin, zartaswar shirin raya harkokin masana'antu na SADC ya kasance wani muhimmin matakin da aka samu wajen gudanar da aikin din, haka kuma, idan za a iya aiwatar da shirin yadda ya kamata, babu shakka, zai samar da kyawawan damammaki sosai ga kasashen yankin da kuma shiyya-shiyya wajen kyautata tsarin tattalin arzikin SADC.

A watan Afrilu na bana, an zartas da shirin raya harkokin masana'antu na SADC dake mai da hankali kan raya ayyukan masana'antu, karfafa kwarewa kan aikin da kuma neman dunkulewar yankin, a yayin taron shugabanni na musannan na SADC da aka yi a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe.

A wannan taron kuma, shugaban kasar Botswana Seretse Khama Ian Khama ya kama aikin shugaban karbar-karbar kungiyar SADC na wani sabon zagaye inda ya maye gurbin tsohon shugaban kungiyar, watau shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe.

Kana shugaba Khama ya bayyana cewa, kasashe marasa bunkasuwar tattalin arziki a wannan yanki za su iya neman taimako daga kasashen da suka fi samun bunkasuwar tattalin arziki a yankin, ta yadda za su iya kyautata karfinsu na samar da kayayyaki, haka kuma, yana fatan za a iya cimma wani kudurin da zai taimaka wa gwamnatocin da abin ya shafa wajen aiwatar da shirin raya harkokin masana'antu na SADC yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China